Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: wata gobara na ci gaba da bazuwa a tsaunukan birnin Kudus da aka mamaye, kuma an kwashe wasu mazauna yahudawan sahyoniya da ke cikin wadannan yankuna da aka mamaye sakamakon bazuwar wutar.

30 Afirilu 2025 - 21:37
Source: ABNA24

Tashar ta 12 ta Hebrew: Mazauna matsugunai 9 a yammacin Kudus sun tsere saboda gobara.

Mazauna 10,000 sun tsere daga wutar gobarar, An bayar da rahoton cewa, dubban yahudawan sahyoniya bayan gobarar da ake ci gaba da yi a birnin Kudus, tare da kwashe mutane daga asibitoci tare da makalewa ma'aikatan kashe gobara a cikin wani zobe na wuta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha